Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Alhaji Bello Hamza, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
- An Dakatar Da Bin Uthman Daga Limancin Masallacin Sahaba, DSS Ta Gayyace Shi
- Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano
Sako daga Sagir Ibrahim
Assalamu alaikum, ‘yan uwa da abokan arziki ina muku Sallama irin ta addinin Musulunci!Â
Ina mika sakon gaisu ga iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki tare da fatan alkhairi, da fatan mun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya sa mu ga ta wani sati da alkhairi.
Sako daga Zara Murtala
Ina mika sakon gaisuwata ga Iyayena da yayyena da kannena ‘yan uwana mata da maza wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an yi Sallah Juma’a lafiya.
Sako daga Nana Asma’u Musa
Assalaikum alaikum
Ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na ina musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan, sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannan su tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Zubeda Muhammad
Assalamu alaikum, ina gaida iyayena da mijina da ‘yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa ina muku fatan alkhairi da fatan kun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin.
Sako daga Rahina Hashim Amar
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana smin ya Allah.
Sako daga Zuwaira Ahmad
Assalamu alaikum, Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan gidan wannan jarida mai albarka na LEADERSHIP Hausa tare da mika godiya ta da suka bani dama na mika sakon gaishe- gashena na gode.
Ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina da iyayena ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Fatima Suleiman
Assalamu alaikum! Ina mika sako gaisuwata ga mutanen gidan wannan jarida mai albarka tare da mika godiya ta da suka bani dama na mika sakon gaisuwata.
Ina gaida Iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abokan karatu da abokan aiki na da al’ummar Musulmi baki daya tare da barka da Juma’a da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Yusuf Makaddas
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga mamata ina mata data alkhairi da fatan Allah ya ja da kwana, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya.
Ina mika sakon gaisuwata ga matata da ‘ya’yana ina musu fatan alkhairi. Ina gaida iyaye wato yayyen iyayena da kannansu, ina gaida kannena , ina gaida abokan arziki na kusa da na nesa, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.