Assalamu Alaikum. Wannan sako ne daga gare ni zuwa gare ku mahaifana, na tabbata yana da matukar muhimmanci ku karanta shi da zuciyar fahimta, kuma ku yi dogon nazari a kan wannan maudu’in, ku dauke shi a matsayin abinda zuciyata take fada maku ba wai bakina ba!
Mahaifana!
Wayi gari a cikin wani zamani mai cike da rudu da hayaniya mai rusa tarbiyyar manya da yara, maza da mata, matasa da dattijai, abin da ya sa sanya ake ta samun matsaloli masu muni a alakar tsakanin namiji da mace.
Yanzu manya da yara maza da mata tunaninsu ya riga ya karkata ne a abinda ya shafi alakar namiji da mace cewa babu wata mu’amala tsakanin namiji da mace in ba mu’amalar jinsi ko kwanciya ba, wannan tunanin tsari ne na turawa da suka yi shirin dakushe tunanin al’umma da kuma raunata ilimi da sanin ya kamatansu domin ci gaba da mulkarsu har a cikin tunaninsu.
Sanannan abu ne a wajen masu mulkin mallaka cewa, matukar kana son ka mulki al’umma to dole ne ka fara lalata tarbiyyar cikin gida wato iyali, sai ka lalata musu tunanin yadda suke kallon zamantakewa, sai ka sanya masu wani tunani da yake rinjayarsu da shagaltar da su daga yin tunani a kanka, idan kuma kana son family ya yi saurin rushewa to kawai ka lalata tarbiyyar mace, idan ka kasa lalata masu tarbiyyarta kuma to ka yi kokarin hana ta tsayuwa da ayyukanta na uwa.
Rubuce-rubuce ko kuma fina-finan batsa sune babban tsarin cikin ruwan sanyi da turawa suka kirkira domin lalata tarbiyyar iyali, da kuma tarbiyyar mace musamman, shi wannan tsarin ya fara samo asali tun karni na sha bakwai a kidayar miladiyya a shekarar 1748, wanda wani mutum mai suna Fanny Hill dan kasar Ingila ya fara rubuta littafin nobel na batsa na farko, wanda a lokacin ma har gwamnatin kasa sai da ta haramta mallaka, seya da seyar da littafin tare da sanya doka mai tsanani ga duk wanda aka kama da littafin saboda hatsari da matsalolin da ta hango ga al’ummarta ta bangaren tunani da kuma shirin ruguza al’umma baki daya.
Tsarin ya ci gaba da tafiya ta hanyar samar da wadannan rubuce rubucen har zuwa karni na sha tara, inda aka fara samun wannan abin a matsayin shirin film bayan da aka samu fasahar daukar hoto mai motsi, har dai zuwa wannan lokacin da abin yake dada mamaye duniya.
Tsarin yin wasan kwaikwayo na bayyana tsiraici da mu’amalar jinsi tsakanin namiji da mace dadadden abu ne a cikin al’ummar Rumawa da wasu sassa na turai kamar Girka da Faransa, amma a tarihin nahiyar Afrika babu wannan mu’amalar da sunan wasan kwaikwayo.
Ya mahaifana masu daraja!
Na yi wannan shimfidar ne saboda in sanar da mu irin hadarin da wannan masana’antar ta fina-finai da rubuce-rubucen batsa a takaice.
Nasarar masu shirya wadancan fina-finan shekarun baya a zukatan matasa da ma dattijai maza da mata na al’ummarmu, saboda rahoton PornHub babban shafin masana’antar fina-finan batsa ya tabbatar da cewa a shekarar 2021 zuwa yau Nigeria ce kasa ta farko a kallon fina-finan batsa, Ghana makociyar ita ce ta biyu!
Ba burina tsawaitawa a wadannan babin ba, abinda nake so shi ne ku fahimci abinda ke yawo a kwakwalwata, ku fahimci ina matsalar ta samo asali da kuma warwarar zaren domin gujewa matsatsalu da suka addabemu na zinace-zinace da ayyukan ash’sha.
To amma me ya janyo wannan karkatar da al’ummarmu zuwa ga wannan aikin?
Da farko, zamaninmu ya bambanta da zamaninku ya Mahaifana, ginin jiki da kirarmu daban da taku, kuma babu abinda zai sa mu zamo daya ta kowanne fanni.
Mafi yawan abincin da muke ci yanzu abinci ne mai matukar gina sha’awa a cikin kankanin lokaci, abin sha kuma dama abu ne mai matukar cakuduwa da sinadaran girmama sha’awa da kuma kassara tunanin yaro, dukkan abinda jikinmu ya ginu da shi ba komai bane face zallaln abinci mai kusanto da girman yaro da bashi karfin sha’awa, a takaice zan iya cewa maganadisun sha’awa ne!
Kun ga jikinmu da wannan abincin ya ginu, yanzu mun girma, muna jin tasirin wannan abincin da muka girma ta dalilinsa, kuma muna fama da wannan tsananin sha’awar da jikinmu ya ginu a kanta, ba wai son ranmu bane ya mahaifana! Wallahi jikinmu ne a haka!
A lokacin da ya kamata ku bamu kariya a kan sarrafa sha’awarmu cikin da’ar ubangiji, sai kuma kuka barmu da son zuciyarmu da kuma karamar kwakwalwarmu da bata san komai ba sai wannan sha’awar da ta ginu a kai, kun kasa jan hannunmu domin shiryar damu, kun tauye hannu sosai wajen bamu abinda zai yi daidai da kirar halittar da kuka dora mu a kai!
Muna kokari duk da haka wajen samun rufawa kanmu asiri ta hanyar yin aure da kare al’aurarmu, amma a wannan lokacin kuma sai kuka tsananta mana lamarin aure, ta kai idan mutum ya furta kalmar aure zai yi to kamar ya taro wa kansa fada da duniya baki daya!
Mahaifana!
Dadanku mata kuma, suma kamar dai mu mazan haka suke, dukkan kirar jikinsu da namu da irin abinci daya dai ta ginu, maimakon ku taimake su wajen kare kansu ta hanyar saukaka lamarin aurensu, kun fifita ku aurar da su ga mai kyale-kyalen duniya da ku baiwa talaka, kun fifita idan kun yi masu aure bakin ciki ya kashe su, kun fifita shaidan ya ribace su ya ingiza su yin zina alhali suna da aure! Kun fifita su rika mu’amala da samarinsu da kuka ki bari su aura alhali suna dakin aure!
Shin me za ku gaya wa Allah a kan hakkinmu da ke wuyanku? Shin Allah zai kyale ku? Shin kuna ganin abinda kuke aikatawa daidai ne?
A lokacin da kuka hana mu kame kanmu daga fadawa halaka, sai kuma aka samu wadannan turawan suka bijiro mana da abinda yake daidai da bukatar zuciyarmu, suka rika ribatar zukatanmu da kuma jikinmu wajen bayyana mana abinda zuciyarmu ke dauka jin dadi ne!
Rayuwar duniya ya ku mahaifana fada ne tsakanin rundunar shaidan da son zuciya da rundunar Allah mai horo da alkhairi, wani lokacin idan mun iya kare kanmu daga kalle-kallen banza, kuna tunanin wani lokacin za mu iya? Wanda da ace kun saukaka mana da hakan bata faru ba!
Mahaifana masu daraja!
Bani da buri a rayuwata da ya wuce na faranta maku rai, bani da nufin sanya ku cikin yanayin bacin rai da kunci, saboda na san kun yi dawainiya kun sha fama da ni, kuma babu abinda zan yi na iya sauke hakkinku da ke kaina, kamar yadda kuma na san babu abinda kuke da buri face ku ga na rayu rayuwa mai kyau, mai cike da farin ciki da yiwa ubangiji da’a, na sani ba burinku cutar da ni ba ko kadan.
Ya mahaifana!
Ni dan adam ne kamar kowa, zan iya yin dai-dai kuma zan iya yin kuskure, kamar yadda ruhin yi maku biyayya yake tare da ni haka zalika a hannu daya kuma akwai wata zuciya mai horo da mummuna da ke ingiza ni zuwa ga aikata abinda baku tarbiyyantar da ni da shi ba, wani lokacin idan na yi nasara mahaifana wani lokacin ban san me zai iya faruwa ba!
Ni wani nauyi ne da Allah ya dora maku a rayuwar duniya, kuma ku abin tambaya ne a kan irin kariyar da kuka bani daga fadawa tarkon son zuciya, ina gama ku da Allah, ku zamo sanadin tsirar imanina da rayuwata wajen katange ni daga fadawa wannan halakar da ke neman kassara imanina da ruhina!
Mahaifana masu daraja!
Na san za ku iya cewa in lizimci azumi hakan yana kawo maganin wannan abin da yake damu na!
Gaskiyar Magana azumi ba abinda yake yi a wannan zamanin na daga rage wannan lamarin, saboda a haka jikina da duk dan zamanina ya ginu, bani da wannan karfin danne abinda ke takura min ta hanyar azumi, ba kuma ina yi maku karya ba ne, wallahi gaskiya nake fada maku.
Idan kuna ganin la’alla ban yi hankalin da za ku min aure ba, to ku dubi bangaren halakar da zan iya fadawa sanadin rashin yin hakan, kuma ku tuna cewa magabata da kananun shekaru iyayensu suke yi masu aure domin hana su afkawa wani tunani na daban da zai iya sabbaba samun da irin matsalar da muke fama da ita a wannan zamanin, dan abin da kuke ganin ban sani ba a game da zamantakewar aure, ku zaunar da ni ku sanar da ni, ku fahimtar da ni ku ceci rayuwata!
Fatan za ku yi nazarin maganata, ina kaunar ku mahaifana!