Ministan ma’adanai, Dr Dele Alake, ya bayyana cewa, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule yana bayar da cikakken goyon baya don ganin an samu cin gajiyar ma’adanan da Allah ya shinfida a jihar.
Ministan ya kuma ce, jihar Nasarawa tana a kan gaba wajen hada hannun da gwamnatin tarayya don ganin an bunkasa banmgaren ma’adanai a jihar dama kasar baki daya.
Wadannan bayanan sun fito ne daga takardar sanarwar da mai ba ministan shawarar a kan al’amurran watsa labarai, Segun Tomori ya raba wa manema labarai, ya kuma kara da cewa, Gwamnan jihar Nsarawa yana bayar da gudumawa wajen ganin an kafa ma’aikatar hako ma’adanin ‘Lithium’ a jihar, wanda zai taimaka wajden bunkasar tattalin arzikin Nijeriya baki daya.
“Gwamnan yana bayar da gudummwa ganin an bunkasa bangaren ma’adanai ba wai don jiharsa ce keda ma’adanai kala-kala ba amma don shi da kansa injiniya ne da yake da masaniya a kan abin da ya shafi harkar ma’adanai. Ya san yadda abubuwa ke tafiya a bangaren, na yaba masa kwarari da gaske a kan haka” in ji Alake.