Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Talata, ya kaddamar da sabbin kwamishinoni 18 da za su zama majalisar zartarwa ta jihar tare da raba wa kowanne Ma’aikatar da zai jagoranta.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a dakin taro na gidan gwamnatin da ke Gusau, babban birnin Jihar.
Babban alkalin jihar Zamfara, Mai shari’a Kulu Aliyu ce ta rantsar da sabbin kwamishinonin.
A jawabinsa, “Gwamna Dauda Lawal ya umurci sabbin kwamishinonin da aka rantsar da su rubanya kokarinsu domin za a tantance su ne ta ci gaban da suka kawo a Ma’aikatunsu.”
Gwamna Lawal ya yi kira ga kwamishinonin da su samar da kyakkyawar alaka a tsakanin ma’aikatu domin ci gaban jihar Zamfara.
“Gwamna Lawal ya bayyana sunayensu kamar haka: Abdula’aziz Sani Muhammad (SAN) Ma’aikatar Shari’a; Haruna Ya’u , Ma’aikatar Noma; Abdulmalik Gajam Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsari; Abdulrahman Muhammad Tumbido, Ma’aikatar Kasuwanci da masana’antu da yawon bude ido; Mallam Wadatau Madawaki, Ma’aikatar Ilimi da Kimiyya, da Fasaha; Ma’aikatar Muhalli da albarkatun kasa Mahmud Muhammad, Abdullahi Bello Auta, Ma’aikatar Kudi; Dr. Aisha MZ Anka, Ma’aikatar Lafiya.
“Sauran su ne Mannir Haidara, Ma’aikatar Labarai da Al’adu; Hon. Kabiru Moyi , Ma’aikatar Gidaje da Sufayi; Engr. Ahmed Yandi, Ma’aikatar Karamar Hukuma da Masarautu; Sulaiman Adamu Gummi, Ma’aikatar Lamuran Addini; Dr. Nafisa Muhammad Maradun – Ma’aikatar Lamuran Mata da Ci gaban Al’umma; Lawal Barau Ma’aikatar Ayyuka da Kamfanoni; Tasi’u Musa Shinkafi, Ma’aikatar Matasa da wasanni; Amb. Bala Mai Riga, Ma’aikatar Tsaro.
“Akwai ma’aikatu biyu da ke karkashin ofishin Gwamna da ayyuka da dama da suka hada da sa ido kan manufofin gwamnati. Nasiru Ibrahim Zurmi – Sashin aiwatar da Kasafin Kudi na Gwamna; da Salisu Musa Tsafe – Ofishin Agajin gaggawa na Gwamna.”