Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci a bayyana waɗanda ake zargi da kisan ‘yan asalin Kano 16 a garin Uromi, da ke Jihar Edo, a bainar jama’a.
Haka kuma, ya nemi a biya iyalan mamatan diyya.
- Mutane Biyu Sun Mutu, 20 Sun Jikkata A Yamutsin Filin Idi A Gombe
- An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a Kano ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, wanda ya kai ziyara domin jaje.
“Muna godiya ga matakan da aka ɗauka zuwa yanzu, amma dole ne a tabbatar da adalci. Ba wai kawai a ce an yi adalci ba, dole ne mutane su ga an yi adalcin.
“Al’ummar Kano da ma duk ‘yan Nijeriya na buƙatar ganin waɗanda suka aikata wannan kisan gilla sun fuskanci hukunci,” in ji Gwamna Abba.
Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Okpebholo bisa tattaunawarsa da shugabannin al’ummar Hausa a Edo domin hana rikici da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan.
“Biyan diyya da aka alƙawarta abu ne mai kyau, amma dole ne a tabbatar da hakan cikin gaggawa domin taimaka wa iyalan da suka rasa masu ɗaukar nauyinsu,” ya ƙara da cewa.
A nasa ɓangaren, Gwamna Okpebholo ya nuna matuƙar damuwarsa kan wannan kisa, inda ya tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin.
“Ina samu labarin abin da ya faru, na garzaya zuwa Uromi. Na gana da al’ummar Hausa a wajen, kuma mun yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma.
“Ina tabbatar muku da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa,” in ji shi.
Gwamnatin Jihar Kano, ta jaddada buƙatar a tabbatar da adalci domin dawo da kwanciyar hankali da hana aukuwar irin wannan rikici a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp