Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin Jihar na shekarar 2025, da jimillarsu ya kai naira biliyan 719,755,417,663.
Adadin kasafin kudin ya ƙunshi naira 262, 670,66 a matsayin kuɗaɗen da za a kashe na yau da kullum, kashi 36 cikin 100, da kuma 457.08 na ayyukan ci gaba wato kashi 64 cikin 100 na jimillar kudaden.
Idan ba a manta ba a ranar 8 ga watan Disambar 2024 ne Gwamna Abba, ya gabatar da kasafin kuɗin da ya kai naira 549, 160,417,663 a gaban majalisar dokokin jihar, inda daga baya kasafin ya ƙaru da sama da naira biliyan 170.
A kasafin wanda aka yi wa laƙabi da kasafin ƙarfin gwuiwa da ci gaban da kuma bunƙasa Jari da haɓɓaka Tattalin Arziki, gwamnati ta bayar da fifiko ga fannin ilimi da lafiya da samar da ababen more rayuwa da kuma sauran ɓangarori.