Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa marigayin ya kasance mutum mai ɗa’a, da kishin ƙasa da ƙoƙarin ganin ci gaban Nijeriya.
A cikin sakon ta’aziyya da ya fitar ranar 13 ga Yuli, 2025, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa Buhari ya yi rayuwa ta sadaukarwa tun lokacin mulkinsa na Soja har zuwa zama shugaban ƙasa da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya. Ya ce Buhari ya kasance gwarzo da ya tsaya tsayin daka wajen zaman lafiya da ɗorewar haɗin kan ƙasa.
- Mutuwar Buhari Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Kashim Shettima
- Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku
“Shugaba Muhammadu Buhari ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen yi wa ƙasa hidima da gaskiya da riƙon amana. Sauƙin rayuwarsa da jajircewarsa wajen kare talakawa, abubuwa ne da za su ci gaba da kasancewa abin koyi,” in ji Gwamna Yusuf.
Gwamnan ya mika saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, da gwamnatin Jihar Katsina, da ɗaukacin al’ummar Nijeriya. Ya kuma roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya karɓi rayuwarsa cikin rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, da kuma bai wa ‘yan Nijeriya ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp