Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da yunƙurin Kwamishinan ‘Yansandan Jihar na janye jami’an tsaro a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Gwamnan ya bayyana wannan rashin jin daɗin ne yayin da yake jawabi ga al’ummar jihar a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, inda aka gudanar da taron bikin zagayowar ranar ‘yancin kai karo na 65.
Ya bayyana matakin a matsayin “rashin kishin ƙasa” yana mai jaddada cewa irin wannan yunƙuri ka iya barazana ga haɗin kai da nuna ƙaunar juna da ranar ke tunatarwa akai yayin murnar ‘yancin kan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp