Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kaddamar da aikin gina titunan cikin gari mai tsawon kilomita 250 daga yankunan Minna, Bida, Suleja, da Kontagora.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulmalik Sarikin Daji, ya bayar da shawarar gina kofofin karbar haraji a duk manyan titunan.
Bayan kammala shirye-shiryen aikin titunan, gwamnan ya fara da kaddamar da ginin titin Bida Ring Road mai tsawon kilomita 44 a karamar hukumar Bida.
Gwamna Bago ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen kawo sauyi a jihar da kuma kawo sabbin sauye-sauye na zamani da za su bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ya kara da cewa, hanyar Bida Ring Road tana da mahimmanci a cikin ayyukansa na inganta biranen jihar inda ya ce, hanyar za ta inganta ci gaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da inganta rayuwa a yankin.
A nasa jawabin a wajen bikin, Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulmalik Sarikin Daji ya bukaci a sanya kofofin amsar kudin shiga akan manyan titunan da ke cikin jihar.