Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi Allah-wadai da kona cocin Redeemed Christian Church of God da wasu da ake zargin bata-gari ne suka yi a garin Kontagora.
Bago, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Aisha Wakaso, ta fitar a ranar Lahadi a Minna, ya bayyana harin da aka kai wa Cocin a matsayin “rashin hankali”.
- Kwalekwale Ya Kife Da Fasinjoji 40 A Sakkwato
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojoji Sun Ƙona Motocin Sintiri 2 A Sakkwato
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, wasu da ake zargin bata-gari ne da sanyin safiyar Asabar sun yi awon gaba da wasu kayayyaki tare da kona Cocin da ke kan hanyar Kwalejin Ilimi ta Tarayya, FCE a Kontagora.
Ya ce, wannan danyen aikin na kone-kone da sace-sace da aka yi wa Cocin ba wai hari ne kawai ga al’ummar Kirista ba, illa hari ne kai tsaye ga zaman lafiya da hadin kan da ake da shi a jihar.