Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sauke babban basarake kuma Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, Alhaji Abdulrazak Isa Koto, tare da wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Bello ya bayyana Alhaji Ahmed Tijani Anaje, wanda shi ne OHI na OKENWE a matsayin sabon Ohinoyi na Ebiraland.
- 2024: Gidauniya Ta Tallafa Wa Zawarawa Da Kayan Masarufi Da Kudi A Kaduna
- Xi Ya Jaddada Bukatar Samun Cikakkiyar Nasara Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
An sanar da sauke Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, wanda kuma shi ne shugaban majalisar gargajiya ta Lokoja/Kogi a ranar Litinin a taron majalisar zartaswa ta jihar da aka gudanar a dakin taro na Exco na gidan gwamnati da ke Lokoja.
Gwamna Bello a lokacin da yake sanar da sauke sarakunan, ya ce, “Bayan bin dokokin da suka kafa masarautun gargajiya, da dokoki da ka’idojin da suka dace, mun cimma matsaya kamar haka:
“An sauke Mai Martaba, Alhaji Abdulrazaq Isah Koto, Ohimege-Igu Koton-Karfe, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Gargajiya ta Karamar Hukumar Lokoja/Kogi, an mai da shi zuwa Karamar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.
“An sauke Mai Martaba, Sam Bola Ojoa, Olu Magongo na Magongo, an mai da shi zuwa garin Salka, karamar hukumar Magama ta Jihar Neja.
“An sauke mai martaba, Samuel Adayi Onimisi, Obobanyi na Emani, an mai da shi zuwa Doko, karamar hukumar Lavun ta jihar Neja.”