ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Buni Ba Zai Shiga Hadakar Jam’iyyun Adawa ba – Mai Magana Da Yawunsa

by Muhammad Maitela and Sulaiman
7 months ago
Buni

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya karyata jita-jitar shiga tawagar hadakar jam’iyyun adawa, wadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Alh. Atiku Abubakar yake jagoranta.   

Bayanin hakan ya zo ne kunshe a cikin wata sanarwar manema labaru, wadda mai magana da yawun Gwamna Buni, Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu ranar Asabar.

ADVERTISEMENT
  • Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
  • ‘Yansanda Sun Ƙwato Bindigogi Da Tabar Wiwi A Zamfara Bayan Artabu Da ‘Yan Bindiga

Wakilinmu a jihar Yobe ya nakalto cewa, akwai wani sakon wayar tafi-da-gidanka da ke yaduwa, inda aka yi ikirarin cewa Gwamna Buni da wasu gwamnonin APC guda huɗu sun yanke shawarar shiga jam’iyyar PDP kafin zabukan 2027.

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi.

Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya gano ra’ayinsa ko ya iya hasashen yanayin siyasarsa.

“Gwamna Buni bai tsaya kawai dan jam’iyyar APC ba; ko kawai gwamnan APC ba. Shi ne APC gaba dayanta, saboda sanannen abu ne cewa APC ta ratsa jijiyoyin jininsa.

“Sannan gudunmawar da ya bayar wajen gina APC a matsayinsa na Sakatarenta na kasa sau biyu, kuma ya rike ragamar Shugaban kwamitin tsara taron jam’iyyar; ya bambanta shi da sauran yayan jam’iyyar, kuma ba abu bane mai yuwa ba ace ya bar jam’iyyar.” In ji shi.

Mai magana da yawun Gwamnan ya ce, marubucin sakon tare da masu daukar nauyinsa, ko shakka babu, yanayin salon siyasar Gwamna Buni ya na burgesu, sannan suna burin kasancewa irinsa, “amma kawai, wannan ya na iya zama kawa-zuci.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
Manyan Labarai

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
Manyan Labarai

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Next Post
Yadda Za A Gudanar Da Zaben Sabon Paparoma Da Zai Gaji ‘Pope Francis’

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.