• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Fara Rabon Tallafi A Jihar Zamfara

Rabon Ba Na Siyasa Ba Ne, Kowa Zai Amfana

by Leadership Hausa
2 years ago
Zamfara

Gwamna Dauda Lawal, a ranar Talata ya ƙaddamar da rabon kayan abinci a matsayin tallafi ga al’ummar Jihar Zamfara.

Yayin ƙaddamar da wannan bayar da tallafi, Gwamna Lawal ya yi kira ga kwamitin da ke da alhakin rabon tallafin da su yi aiki tsakaninsu da Allah.

  • Gwamna Dauda Ya Karbi ‘Yan Mata Hudu Da Suka Kwashe Watanin 7 A Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara
  • Gwamnatin Zamfara Ta Bada Umurnin Ɗaukar ‘Yan Sa-kai

Mai magana da yawun gwamnan na Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Gusau, ya ce wannan tallafi na daga cikin matakan farko don ragewa mutane raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana za ta ba jihohi bashin Naira Biliyan 5.

Takardar ta ci gaba da cewa: “A jawabinsa yayin ƙaddamar da tallafin, Gwamna Lawal ya ja hankalin membobin wannan kwamiti da su sa tsoron Allah gaba da komi.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

Jerin Gwarazan Taurarinmu

Cikin jawabin, gwamnan ya ce gwamnatin Zamfara za ta ɗauki mataki a kan duk wani wanda aka kama da laifin karkatar da wannan tallafi.

A cikin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta ce za ta ba jihohi bashi, Jihar Zamfara ta samu Naira biliyan biyu, da buhun shinkafa dubu 11, 877 da kuma buhun shinkafa 2, 834, wanda za ta raba su ga ƙananan hukumomi shida.

Sashe na biyu na wannan tallafi za a gabatar da shi ga ƙananan hukumomi takwas wanda za a fara da zaran gwamnatin ta amshi wannan tallafi daga gwamnatin tarayya.

Mataimakin Gwamna, Mallam Mani Mallam Mummuni shi ne zai jagoranci kwamitin da zai yi wannan rabon tallafi ga al’umma.

Kowacce ƙaramar hukuma za ta samu buhun shinkafa 2, 000. Buhunan Taki da amfanin gona.

Haka kuma gwamnatin za ta fara bayar da tallafin karatu ga ɗalibai ‘Yan asalin jihar Zamfara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Manyan Labarai

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu
Manyan Labarai

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Manyan Labarai

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Next Post
Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas

LABARAI MASU NASABA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.