Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci sabbin manyan sakatarorin da aka naɗa a jihar da su gudanar da ayyukansu bisa ƙa’idojin aikin gwamnati, dokokin kula da kuɗaɗen gwamnati da sauran dokokin da suka shafi aikinsu.
Gwamnan ya yi wannan kira ne ranar Alhamis, lokacin da ya rantsar da sabbin manyan sakatarori biyar na Ma’aikatan Gwamnatin Jihar a babban zauren Gidan Gwamnati da ke Gusau.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar 22 ga Oktoba, 2026, ta bayyana cewa rantsar da sabbin manyan sakatarorin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa tsarin gudanarwa da inganta ayyukan ma’aikatan gwamnati a jihar.
Waɗanda aka rantsar ɗin su ne Ahmad S. Zamfara, Nasiru Halilu Anka, Mu’azu Jibril Guraguri, Adamu Abdullahi Kanoma da Sani Muhammad Shinkafi.
Babban Alƙalin Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu, ce ta jagoranci rantsar da su, inda suka yi alƙawarin kasancewa masu aminci da biyayya ga Tarayyar Nijeriya bisa tanadin kundin tsarin mulki da sauran dokokin ƙasa.
Da yake jawabi a wajen bikin rantsarwar, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa hukumomin gwamnati, tare da tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati suna da ƙwararrun shugabanni masu ilimi, ƙwarewa da ladabi da ake buƙata domin cimma burin ci gaban jihar.
Gwamnan ya taya sabbin manyan sakatarorin murna, yana mai cewa naɗin nasu ya nuna amincewar gwamnati da ƙwarewarsu, gogewarsu da kuma shirinsu na ɗaukar manyan nauye-nauyen da ke gabansu.
Ya ce, “Zama babban sakatare ba ci gaban mutum ne kawai a matsayinsa na ma’aikaci ba. A matsayinku na manyan jami’an gudanarwa, yadda kuke yanke shawara da kuma yadda kuke gudanar da ayyukanku na da tasiri kai tsaye ga ingancin aikin gwamnati da walwalar al’ummar da muke yi wa hidima.
“Babban sakatare na da muhimmiyar rawa a gwamnati, domin shi ne ke jagorantar harkokin gudanarwa, tabbatar da dorewar ayyukan ma’aikata da kuma bayar da shawarwari kan manufofin gwamnati. Haka kuma, yana kula da ladabi, daidaita ayyukan ma’aikatarsa da tabbatar da cewa ana amfani da dukiyar gwamnati bisa manufar da aka ware ta dominta.”
Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta hau mulki ne da ƙudirin inganta shugabanci, ƙarfafa hukumomin gwamnati da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da za su biya buƙatu da muradun al’ummar Zamfara.
Ya ce ana ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin inganta harkokin gudanar da gwamnati da samar da muhimman ayyuka ga jama’a, inda ma’aikatan gwamnati suke taka muhimmiyar rawa wajen mayar da manufofi da shawarwarin gwamnati zuwa ayyukan da jama’a za su amfana da su.
Gwamnan ya kuma buƙaci sabbin manyan sakatarorin da su gudanar da ayyukansu bisa cikakken fahimtar manyan manufofi da abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
Ya jaddada cewa ya kamata a riƙa tsara manufofi da shirye-shirye yadda ya kamata, samar da dabarun aiwatar da su masu ma’ana, sa ido kan yadda ake gudanar da su da kuma tantance sakamakon da ake samu a kai a kai.
Haka kuma, ya buƙaci su ƙulla kyakkyawar alaƙar aiki da kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, tare da mutunta nauyin da kowane ɓangare ke da shi.
A cewarsa, shugabannin siyasa su ne ke tsara manufofin gwamnati, yayin da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati ke bayar da ilimin hukumomi, shawarwarin fasaha da ƙwarewar gudanarwa da ake buƙata domin aiwatar da manufofin.
Gwamna Lawal ya ce waɗannan ayyuka suna haɗa juna ne, kuma nasarar gwamnati wajen gudanar da ayyukanta tana dogara ne da mutunta juna da kyakkyawar fahimtar da ke tsakanin shugabannin siyasa da ma’aikatan gwamnati.












