Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Darakta Janar na Hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwar Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta Ƙasa (National Institute for Security Studies NISS) da ke Abuja.
Daraktar Sadarwa da Hulɗa ta Cibiyar NISS, Lilian Omo-Odigwe, ce ta tabbatar da wannan naɗi a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2026. Ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da naɗin ne biyo bayan shawarar da Darakta Janar na DSS mai ci a yanzu, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya gabatar masa.
Naɗin na Bichi zai ɗauki tsawon wa’adin farko na shekaru huɗu wanda ya fara aiki nan take daga ranar 22 ga watan Oktoba, 2026, bisa tanadin sashi na 4 na Dokar da ta Kafa Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta Ƙasa ta shekarar 2019. Bichi zai maye gurbin Mista A.A. Gadzama (OFR, mni) a matsayin shugaban hukumar gudanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa Bichi wanda ya miƙa ragamar jagorancin hukumar DSS ga Ajayi a watan Agustan 2024 ya fara aikin tsaro ne a sashin Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano kafin mayar da aikinsa zuwa matakin tarayya a shekarar 1984.
Cibiyar ta bayyana cewa zuwan Bichi zai ba da gagarumar gudunmawa wajen inganta aikin cibiyar sakamakon ɗumbin ƙwarewar da yake da ita a fannin leƙen asiri, da dabarun tsaro, da shugabanci, da kuma bayar da horo ga jami’an tsaro.













