Gwamna Dauda Lawal ya rantsar da Yakubu Sani Haidara a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar Zamfara, tare da sabbin Sakatarorin Dindindin 12.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a tsohon zauren Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau. Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa an kuma ƙirƙiri sabon ofishi mai kula da ayyukan ƙungiyoyin tallafi da shirye-shiryen ci gaba, wanda zai riƙa aiki kai tsaye da gwamna.
- Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara
Gwamna Lawal ya bayyana sabon Shugaban Ma’aikata a matsayin gogaggen jami’in gwamnati da ke da ƙwarewa a harkokin gudanarwa na sama da shekaru 30. Ya buƙace shi da sabbin Sakatarorin dindindin da su jajirce wajen aiwatar da manufofin gwamnati cikin ƙwarewa da gaskiya.
Ya kuma jaddada cewa an zabo sabbin Sakatarorin dindindin ne ta hanyar tsari mai inganci da ke tafiya da ƙa’idojin zamani, wanda ya haɗa da gwajin basira, da jarrabawar rubutu, da tantancewar ƙwararru.
Gwamnan ya buƙaci sabbin sakatarorin da su yi aiki da dabaru da nagarta, tare da tabbatar da cewa ayyukan da ke hannunsu na tafiya da ajandar gwamnatin sa guda shida, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Zamfara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp