Gwamnatin Jihar Katsina na duba yiyuwar sake tsarin kasuwar Fatima Baika da aka fi sani da Santara a Katsina.
Hakan na da nufin ba da dama ga masu gudanar da kasuwanci iri daya su kasance a layi daya a cikin kasuwar.
- Sin Za Ta Kaddamar Da Gangamin Yayata Ci Gaban Mata
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
Kwamishnan kasa da sifiyo, Dakta Faisal Umar Kaita ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ya gabata.
Dakta Faisa ya ce majalisar zartarwar jihar ta amince da sake tsarin tare da yin amfani da shawarar kwamitin da aka kafa kan sake tsarin kasuwar.
Haka kuma ya ce za a rushe duk wani gini da aka yi ba kan ka’ida ba domin samun kyakkyawan yanayin gudanar da kasuwanci.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa an amince da samar wa ‘yan kasuwar da aka rusa wa shaguna matsuguni mai kyau.
Haka kuma majalisar zartaswa ta yanke hukuncin cewa yanzu a jihar iyaye na da damar zabar jarabawar daya da gwamnati za ta biya wa daliban ajin karshe na sakandire.