Gwamnan da ke kan kujerar gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya lashe zaben tikitin tsayawa takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar PDP a babban zaben da ke tafe.Â
PDP ta gudanar da zaben fitar da gwani ne a ranar Laraba a garin Yenahoa babban birnin jihar.
Da ya ke ayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin PDP na gwamnan Jihar Bayelsa, gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ce Sanata Diri ya samu nasara ne da kuri’u 305 da ya janyo masa lashe zaben.
A cewarsa, adadin wakilan jam’iyyar 315 ne aka tantance yayin da 313 kuma suka samu damar kada kuri’arsu.
A cewar shugaban kwamitin zaben, “Bayan gamsuwa da cika sharudan kashe zabe tare da samun mafi rinjayen kuri’u, ni Sanata Ademola Jackson Adeleke bisa dogaro da karfin iKon da aka ba ni a matsayina na shugaba Kuma babban jami’in tattara sakamakon zaben, a kan hakan, na ayyana Sanata Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zaben.
“Kan hakan ya sake samun damar lashe tikitin zaben PDP a zaben gwamna da za a gudanar a watan Nuwamban 2023.”
Da ya ke jawabin godiya, gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Diri, ya ce zaben fitar da gwanin PDP ya kasance zabe mafi inganci a jihar, ya kuma kara da cewa jam’iyyar za ta cigaba da yin tasiri a jihar.
Ya nuna kwarin guiwar sa na cewa jam’iyyar za ta yi nasara a babban zaben gwamnan Jihar da ke tafe.