Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya nuna jin daɗinsa tare da karrama Kocin Super Falcons, Justin Madugu, bisa nasarar da ya samu wajen jagorantar ‘yan wasan ƙwallon ƙafa na mata na Nijeriya zuwa ga nasara a gasar cin kofin Afrika ta mata (WAFCON) da aka gudanar a Morocco.
Madugu, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Numan a jihar Adamawa, ya samu kyautar gida mai ɗakuna uku da kuma Naira miliyan 50 a wani biki na musamman da aka shirya a gidan gwamnati da ke Yola.
- Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
- Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
A yayin bikin, Gwamna Fintiri ya yaba da jajircewa da ƙwarewar Madugu wajen horar da ƙungiyar har zuwa samun wannan nasara ta tarihi. Ya ce, “Tun daga lokacin da aka naɗa shi a matsayin Kocin Super Falcons, ban taɓa shakkar cancantarsa ba. Hazaƙarsa da kishin ƙasa sun taimaka wajen ganin Nijeriya ta lashe gasar WAFCON karo na goma.”
Gwamnan ya bayyana cewa wannan nasara ba wai ga Nijeriya kaɗai ta tsaya ba, har da jihar Adamawa gaba ɗaya, kasancewar ɗaya daga cikin ƴaƴanta ne ya taka rawar gani a matakin ƙasa da nahiyar Afrika. Fintiri ya ce hakan wata shaida ce ta yadda jihar ke da haziƙai da suka dace a ba su dama don su ci gaba da wakiltar Nijeriya.
Baya ga karramawar, Gwamna Fintiri ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da inganta wasanni a faɗin jihar. Ya bayyana cewa an riga an gina filayen wasa na zamani a wasu ƙananan hukumomi, tare da wani babban filin wasa na ƙasa da ƙasa da ake ci gaba da ginawa domin bai wa matasa damar nuna basirarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp