Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya nada, Hussaini Abubakar-Giro, a matsayin mamba a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, don maye gurbin mahaifinsa, Sheik Abubakar Giro, wanda ya rasu a ranar Laraba.
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’iqamatus Sunnah ta kasa (JIBWIS) ta kasa ta roki Gwamnan da ya duba daya daga cikin ‘ya’yan marigayin kan mukamin da aka bai wa mahaifinsu wanda Gwamnan ya amince da hakan.
- Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Babban Malamin Addinin Musulunci Giro Argungu
- NUJ Kebbi Ta Yi Alhini Rasuwar Tsohon dan Jarida Ibrahim Argungu
Alhaji Ahmed Idris, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Ahmed Idris ya bayyana cewa gwamnan ya amince da nadin ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar (JIBWIS) karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Sheik Abdullahi Bala-Lau, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Gwamnan ya tabbatar wa kungiyar Izalar cewa an riga an karbi wannan kiran.
Idris ya godewa kungiyar bisa wannan ziyarar, inda ya ce: “Rashin ba ga iyalansa kadai ya shafa ba har kowa da kowa.”
Ya ce Abubakar Giro wani ginshiki ne na yada addinin Musulunci a kasashen Afirka da dama, ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya gafarta masa kurakuransa, ya karbi ayyukansa na alheri, ya saka masa da Jannatul Firdaus.
Malaman sun kuma gabatar da addu’o’i na musamman ga marigayin, da sauran musulmin da suka rasu tare da addu’ar samun zaman lafiya a dukkan sassan Nijeriya.