Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da sakin fiye da naira biliyan 1 da miliyan 300 don biyan bashin ma’aikatan kananan hukumomin da suka yi ritaya.
An biya ma’aikatan lananan hukumomi da suka yi ritaya giratuti na karshe ne a 2011.
Gwamnan ya kuma amince da karin girma nan take ga ma’aikatan kananan hukumomi dubu 26, da 85 a fadin kananan hukumomi 11 na jihar.
Daga cikin adadin ma’aikatan da aka karawa girman, dubu 6 da 738 ma’aikata ne na kananan hukumomi, yayin da dubu 16 da 739 kuma malaman LEA, sai dubu 2 da 608 ma’aikatan cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Hon. Ibrahim Dasuki Jalo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, ya bayyana cewar, lokaci na karshe da aka karawa malamai girma a jihar shi ne a shekarar 2009 yayin da aka fara aiwatar da shi a 2014.
Shi ma da ya ke jawabi, kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki, Malam Muhammad Gambo Magaji ya mika takardar amincewar gwamnan jihar na Naira biliyan 1 da miliyan 700 don biyan basussukan ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar a shekarar 2017.
“Biyan bashin ma’aikatan da suka yi ritaya daga gwamnatin Inuwa ya lakume kimanin Naira biliyan 7 da miliyan 900. Idan dai za a iya tunawa, a baya Gwamna Inuwa ya biya bashin kudaden giratutin wadanda suka yi ritaya a jihar na shekarun 2014, da 2015 da 2016 sai kuma yanzu na shekarar 2017, yayin da jimillar kudaden da aka biya a matakin jiha ya kai Naira biliyan 6 da miliyan 600.”