Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana jin daÉ—insa da yadda ake ci gaba da aikin gina filin jirgin saman jihar, tare da wasu muhimman ayyuka a faÉ—in Gusau, babban birnin jihar.
A yau Laraba, gwamnan ya zagaya wuraren da ake gudanar da ayyukan, inda ya duba ci gaban ginin filin jirgin sama, gyaran hanyoyi, sake fasalin sakatariyar jihar, da gyaran makarantu.
- Ramadan: Gwamnatin Sakkwato Ta Rage Wa Ma’aikata Lokacin Aiki
- Afirka Na Da Wata Abokiya Da Za Ta Iya Dogaro Da Ita
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne, ya bayyana cewa gwamnan ya fara wannan rangadi ne tun ranar Talata.
Ya fara da duba babban asibitin Gusau da ake gyarawa tare da ƙara masa kayan aiki.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan duba ayyuka na daga cikin tsarin Gwamna Dauda Lawal na tabbatar da an gudanar da ayyuka masu inganci da kuma kammala su a kan lokaci.
Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp