Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya shaidawa bankin duniya cewa sannu a hankali gwamnatinsa ta samun nasara a yakin da take yi da ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana haka a yayin da ya kai ziyarar aiki ofishin bankin duniya da ke Abuja ranar Juma’a.
- Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara
- Gobara Ta Tashi A Wata Makarantar Allo Ta Hallaka Mutum 17, Ta Jikkata 16 A Zamfara
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan ayyukan raya kasa a fannonin ilimi da kiwon lafiya da sauyi yanayi da bunkasa harkokin noma.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran ziyarar za ta karfafa hadin guiwa a tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da bankin duniya.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafa hadin kulla Alaja da Bankin Duniya.
“Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.”
“Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.”
“Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.”
“Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar samar da isassun kayan aiki da tallafi ga jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.” Cewar Gwamna Dauda
Gwamna Lawal ya baiwa ma’aikatan bankin duniya tabbacin tsaron lafiyarsu a lokacin bayar da tallafi da sanya ido da kuma samar musu masauki da sufuri da dai sauransu.