Gwamnatin jihar Kebbi, a karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta bayar da sanarwar Sauke Sakatarorin Hukumar Ilimi na kananan hukumomi 21 na jihar.
Bayanin hakan na bunshe ne a cikin takardar sanar wa mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Yakubu Bala Tafida, da aka raba wa manema Labarai ta hannun sakataren yada Labarai na Gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Idris Inda takardar ta ce, “Gwamnan jihar kebbi, Dakta Nasir Idris ya amince da sauke dukkan Sakatarorin Hukumar Ilimi na kananan 21 na jihar nan take.
- CBN Ya Soke Cire Kuɗi Kyauta A ATM, Ya Ƙaddamar Da Sabbin Kuɗaɗen Caji
- Kamfanin Harhaɗa Mota Na Dangote Ya Kera Peugeot 3008 GT A Kaduna
“An umurci dukkan Sakatarorin da su mika ragamar shugabancin ga shugabannin sashen kula da tsarin Mulki watau (DPMs)”.
Tafida, ya bayyana godiyar Gwamna Nasir Idris ga Sakatarorin kan irin gudunmuwar da suka bayar ga inganta bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi da kuma goyon baya ga gwamnatinsa a kan jagorancin al’ummar jihar.
Daga karshe, Gwamnan ya gode wa Sakatarorin kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen kawo cigaba a bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi 21 na fadin jihar tare da yi musu fatan alkairi a rayuwarsu ta gaba.