Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya bayyana hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa kan wadanda basu ji basu gani ba a jihar a matsayin rashin hankali.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu-Zango ya raba wa manema labarai a Katsina ranar Laraba.
- Yadda Mahara Suka Kashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama A Wurin Maulidi A Katsina
- Rashin Tsaro: Za Mu Fara Horar Da Jami’an Sa-Kai Don Tsare Al’ummar Zamfara – Gwamna Lawal
A cewarsa, gwamnan ya yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi musamman a kananan hukumomin Musawa, Danmusa, Matazu da Faskari na jihar.
Ya ce, Radda ya yi Allah wadai da hare-haren ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje a garin Musawa, inda ‘yan bindigar suka kashe kimanin mutane 17 a yayin taron Mauludin Annabi Muhammad SAW.
Gwamnan ya sha alwashin kakkabe duk wani ayyukan ‘yan bindigar da ke kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa, a ‘yan makonnin da suka gabata, jami’an hukumar sa ido kan al’umma da aka kafa a jihar sun fatattaki ‘yan bindiga da dama a maboyarsu.
“Wannan ya haifar da shirya hare-haren ramuwar gayya daga ‘yan ta’addan,” in ji shi.