Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya amince da ware wani katafaren fili domin gina Kasuwar kayayyakin gyaran motoci da injina a jihar Kaduna.
Gwamnan, wanda ya sanar da bayar da filin a bikin ranar al’adun kabilar Igbo ta 2024, a ranar Asabar, ya ce hukumar kula da filaye ta Kaduna (KADGIS) tana kan aikin kammala takardun filin.
- Shin Ahmed Musa Zai Iya Dawowa Da Rigarsa A Super Eagles Kuwa?
- Kudi Na Zo Nema A Kannywood Ba Suna Ba -Haruna Talle Fata
Sani ya yi alkawarin cewa, “da kansa zai kaddamar da aikin fara ginin Kasuwar kayayyakin gyaran.”
A cewarsa, gwamnatin Kaduna a shirye take ta hada gwiwa da masu masana’antu da ‘yan kasuwa na Igbo saboda gwamnatinsa ta ba da kwarin gwiwa a fannin sosai.
Gwamnan wanda aka ba wa lakabin sarautar gargajiya na Ezi enyi Ndigbo (abokin kabilar Igbo), ya ce “jihar Kaduna gida ce ga ‘yan kabilar Igbo.”
Ya bayyana ‘yan kabilar Igbo a matsayin mutane na musamman wadanda “masu himma ne, masu kokari, masu juriya, masu kwazo,” ya kara da cewa, suna taimakawa wajen ci gaban Kaduna da ci gaban kasa baki daya.