Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da wani shiri kan yunkurin farfado da hukumar kula da ruwa ta jihar Kaduna da nufin tabbatar da samun tsaftataccen ruwan sha ga ‘yan jihar.
Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar, Dakta Ibrahim Hamza Soba ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kaduna ranar Talata inda ya kara da cewa, gwamnan ya ware fiye da Naira miliyan 600 a watannin Nuwamba da Disamba don samar da ruwan sha.
- Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL
- Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kaduna Uban Kungiya
Soba ya koka da cewa, bayan amsar ragamar mulki a shekarar 2023, gwamnatin ta fuskanci kalubale da dama, amma duk da haka, ta jajirce wajen ganin an magance matsalar karancin ruwan.
Kwamishinan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda aka zuba makudan kudade don ganin an magance matsalar ruwan sha, inda ya ce, gwamnatin baya ta ware kusan dala miliyan 200 a bangaren amma har yanzu ba a shawo kan matsalar samar da ruwan sha ba.