Kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPCL, ya ce yana da sama da lita biliyan 1.5 na man fetur, wanda zai shafe fiye da kwanaki 30.
Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPCL, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- NNPCL Ya Bayyana Ranar Da Matatar Man Fetur Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki
- Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki
Kamfanin ya yi kira ga masu ababen hawa da su kwantar da hankulansu, kamfanin zai ci gaba da rarraba Man a fadin kasar.
“A cikin jerin gidajen mai da muka kai musu sammaci a fadin jihohi da dama, ciki har da Legas da babban birnin tarayya, mun ga layukan sayen fetur din ya ragu, kuma nan ba da jimawa ba, za a nemi sauran layukan a rasa.
“Kamfanin yana so ya bayyana cewa, a halin yanzu, yana da sama da lita biliyan 1.5 na man fetur, wanda zai isa har nan da kwanaki 30.” In ji shi
Talla