Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gargaɗi ‘yan siyasa da ke son tsayawa takarar gwamna su jira lokacin da doka ta tanada kafin su fara yaƙin neman zaɓe.
Ya ce bai dace a fara tayar da kura da yaƙin neman zaɓe tun saura shekaru biyu ba.
- Xi Ya Gana Da Shugaban Zimbabwe Da Na Jamhuriyar Kongo
- Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci
Wannan gargaɗi ya fito ne ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, a wani taron manema labarai da aka yi a Lafia ranar Alhamis.
Gwamna Sule ya tunatar da cewa hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta riga ta fitar da jadawalin da ke nuna lokacin fara yaƙin neman zaɓe.
Saboda haka, a cewarsa bai kamata ‘yan siyasa su yi gaban kansu ba kafin lokacin da INEC ta ƙayyade.
Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar.
Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar.
Ya ce sun ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da shugabannin matasa, sannan an ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakokin jihar domin hana miyagu shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp