Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da aikin tiyatar Ido kyauta ga majinyata 3,600 a asibitin Yusuf Dantsoho (Dutse) da ke cikin jihar Kaduna a ranar Talata 30 ga Janairu, 2024.
Gidauniyar tallafawa ta kasar Qatar da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kaduna ne suka dauki nauyin gudanar da ayyukan domin taimakawa talakawa marasa karfi da ke daf da rasa idanuwansu saboda rashin kudi.
- Fiye Da Mutum Miliyan 5 Ke Fuskantar Barazanar Kamuwa Da Cututtukan Yanayi Da Ake Watsi Da Su A Kaduna
- Bahar: Nasarorin Da Sin Ta Cimma A Fannin Makamashi Mai Tsafta Abin Misali Ne Ga Daukacin Duniya
“Muna godiya ga gidauniyar tallafi ta kasar Qatar saboda ci gaba da tsare-tsare da suke yi a jihar Kaduna. Muna godiya ga gwamnati da jama’ar Qatar saboda taimaka mana wajen magance kalubalenmu.” inji Gwamna Sani
A nasa jawabin, wakilin Gidauniyar kasar Qatar, Dakta Hamdi Abdi, ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa namijin kokarinsa ta yadda ya ke karfafa wa gidauniyar gwiwa wajen gudanar da ayyukan tallafi da ta ke gudanarwa a jihar. Ya kuma nananta cewa, gidauniyar za ta ci gaba da da zuwa jihar Kaduna don gudanar da ayyukanta na tallafi.
Tun a farko a jawabinta, kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Umma K. Ahmed ta bayyana muhimmancin gani da Idanu a matsayin wata baiwa da Ubangiji ya baiwa bayinsa, don haka, kula da ita yake da matukar muhimmanci a rayuwarmu.