Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayar da umarnin gaggauta biyan duk wasu basussukan da Kamfanin Lantarki na Kaduna ke bin Jami’ar Jihar (KASU) daga shekarar 2022 domin maido da wutar lantarki a cibiyoyin Jami’ar da ke Kafanchan da kuma cikin garin Kaduna.
Da jin labarin rashin wutar lantarkin da ake fama da ita a cibiyoyin biyu na Jami’ar, nan take Gwamna Sani ya umarci kwamishinan ilimi, Farfesa Muhammad Sani Bello da ya binciki musabbabin rashin wutar lantarkin a Jami’ar.
- Ofishin Fansho Na Jihar Kaduna Zai Fara Tantance Tsoffin Ma’aikatan Jihar A Ranar Laraba
- Sake Bude Iyaka: Matsalar Da Manoman Arewacin Nijeriya Za Su Fuskanta
Bayan bincike da shawarwarin da Kwamishinan Ilimi ya gabatar, Gwamna Sani ya bayar da umurnin a biya duk basussukan da ake bin Jami’ar daga shekarar 2022 don tabbatar da cewa an dawo da wutar lantarki a cibiyoyin biyu.
Ilimi na daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Gwamna Uba Sani ta sa a gaba, kuma Gwamnan ya ba da tabbacin cewa, za a ci gaba da aiwatar da tsare-tsare don magance kalubalen da dalibai ke fuskanta a dukkan manyan makarantun jihar.