Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da fara aikin gina kananun makarantu 62 a fadin jihar.
Gwamnan a lokacin da yake aza harsashin ginin makarantar sakandare a Nasarawan Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi, ya ce, kafa ginin na wakiltar fara gina makarantu 62 a fadin jihar.
Ya ce manufar gina makarantun shi ne, don tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar shiga ajin karatu.
Gwamnan ya bayyana cewa, a karkashin shirin sabunta kayayyakin more rayuwa na makarantun, za a gina ajujuwa, dakunan gwaje-gwaje, bangaren masu gudanarwa, wurin taro da bandakuna.
Ya kuma ba da tabbacin lura sosai kan cigaban aikin tare da tabbatar da cewa, an gudanar da ingantaccen aiki.
Sanata Uba Sani ya nanata cewa, a jihar Kaduna, karatun Firamare da Sakandare kyauta ne.
Hakazalika Gwamnan ya kaddamar da aikin gina hanya mai tsawon kilomita 25 daga Rigachikun – Tami – Birnin Yero a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani ya ce hanyar idan aka kammala za ta saukaka jigilar kayayyakin amfanin gona daga yankunan karkara zuwa yankunan Birane.
A cewarsa, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, zai kaddamar da aikin gina wasu hanyoyi guda 31 a cikin yankunan karkara na dukkanin kananan hukumomin jihar.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman da kwamishinan ilimi Farfesa Sani Bello da sauran jami’an gwamnati.