• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Ginin Birnin Fasaha Domin Horas Da Matasa 1,600 Duk Shekara 

by Sulaiman
2 years ago
Birnin Fasaha

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da aikin gina birnin koyar da sana’o’i da fasaha a Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi a jihar.

Ya ce, idan aka kammala cibiyar, za ta horas da matasa 400 duk bayan wata Uku-uku, a duk Shekara, za a horas da matasa 1,600 sana’o’i 19 daban-daban.

  • ‘Mutuwar Aminu S. Bono Ta Girgiza Kannywood’
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa

Da yake jawabi yayin kaddamar da ginin a ranar Asabar, Gwamnan ya ce za a sake gina irin birnin a duk fadin mazabun sanatoci uku na tarayya da ke jihar.

Gwamna Uba ya bayyana cewa, wannan kuduri na daga cikin tsarin gwamnatin tarayya na cike gibin da ake da shi a bangaren fasaha da koyar da sana’o’i a tsakanin matasa wanda gwamnatin ta himmatu wajen habbakawa daga kashi 23 zuwa 46 cikin 100 nan da shekarar 2030.

A cewarsa, “A lokacin yakin neman zabenmu, mun yi wa al’ummar jihar Kaduna alkawarin bunkasa ci gaban al’umma domin baiwa matasanmu ilimin fasaha da za su yi gogayya da takwarorinsu na duniya. Da yawan ayyukan da ya dace a baiwa mutanenmu na cikin gida amma sai a mikawa baƙi saboda ƙarancin fasaha. Don haka, mun gano akwai bukatar gaggawa na a sake horas da mutanenmu fasahohi da kirkire-kirkire don su zama abin nema wajen daukar ayyuka.

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Birnin Fasaha
Gwamna Uba sani tare da Mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe da Dan Majalisa Zailani a yayin a za tubalin ginin birnin Fasaha

“Wannan birnin kimiyya da fasaha na Jihar Kaduna da za a gina, za a horas da matasa a fanni daban-daban da ya hada da:

  • Takardar shaidar kwarewa a fannin Kwamfuta na kasa da kasa daga Microsoft Cisco.
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin walda a bangaren man fetur da gas
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin tukin mota.
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin firiji da na’urar sanyi (AC)
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin wutar lantarkin motoci.
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin gyaran motoci
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin dafa abinci
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin walda
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin sanya dandamalin tayels
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin lantarki mai amfani da hasken rana.
  • Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin Aluminiyom
  • Takardar shaidar kwarewa a fanni Ado Da kwalliya.

Anasa jawabin, Sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE), Farfesa Idris Bugaje wanda Darakta a hukumar NBTE, Abbati Mohammed ya wakilta ya ce, wannan shiri na da matukar amfani ga raya matasa wanda hakan zai habbaka tattalin arzikin kasa. Don haka, Gwamna Uba Sani ya cancanci a yaba masa bisa jajircewarsa na gani al’umma ta ci gaba.

Birnin Fasaha

Ginin Birnin zai kasance kamar haka: Dakunan horaswa 16, Dakunan kwanan dalibai guda hudu, ajujuwa, ginin gudanarwar birnin, asibiti, wurin cin abinci, kantina, filin wasan kwallon kwando, filin wasan kwallon kafa, masallaci, dakin janareta, bandakuna da filin ajiye motoci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Na Yafe Wa Aminu S Bono Duka Kudaden Da Nake Bin Sa -Murja Kunya

Na Yafe Wa Aminu S Bono Duka Kudaden Da Nake Bin Sa -Murja Kunya

LABARAI MASU NASABA

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.