Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa, Gwamnatinsa ta kashe makudan kudi da kimaninsu ya kai Naira Biliyan 6,834,564,828.52 wajen gina makarantun kimiyya guda shida yayin da aka samar da kayan aikin da kudinsu ya kai Naira Biliyan 2,536,598,623.89 ga makarantun don inganta harkar Ilimi a jihar.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta wakilci Gwamnan a yayin bikin kaddamar da makarantar sakandaren kimiyya ta mata a Pambeguwa.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 9, Sun Kwato Makamai A Kaduna
- Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Hanyar Tafiyarsu Ta Kai Hari Ga Al’ummar Jihar Kaduna
Bugu da kari, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna, sun duba wasu sabbin ajujuwa da kayayyakin karatu da aka gina a babbar makarantar gwamnati ta Kamfanin Maude da ke karamar hukumar Kubau.
A cewarta, “Wannan makaranta da ke Pambeguwa, tare da makarantun Hunkuyi, Rigachikun, Buruku, Jere, da Manchok, sun nuna gagarumin ci gaba a yunkurin Gwamnati na habbaka ilimin kimiyya gaba a fadin jihar.”
Talla