Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi ta’aziyyar rasuwar Magajin Garin Zazzau – Alhaji Mansur Nuhu Bamalli wanda ya rasu yana da shekaru 53 a safiyar ranar Juma’a bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Mohammed Lawal Shehu ya fitar ta ce, Alhaji Mansur kafin rasuwarsa, yana rike da babbar sarauta a masarautar Zazzau, kuma dan uwa ne ga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
- Na Sha Alwashin Magance Talauci Da Kashi 80 Cikin 100 A Jihata – Gwamnan Kaduna
- Gwamnatin Kaduna Ta Ware Naira Biliyan 3.1 Don Biyan Kuɗin Giratuti
Sanarwar ta ce, marigayin ya rike mukamai da dama a ma’aikatun gwamnatin tarayya da suka hada da shugaban ofishin jakadanci na Nijeriya a kasar Morocco ya kuma rike mukaddashin jakada.
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya da su yi addu’a ga iyalan mamacin a wannan lokaci mai cike da damuwa.
“Gwamnan ya kuma sanar da cewa, an dage duk wasu ayyuka da gwamnan ya tsara gudanarwa a yau Juma’a 20 ga watan Oktoba, 2023, don nuna alhini ga rasuwar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
“Allah (SWT) ya ba shi Jannatul Firdausi, kuma Ya gafarta masa kura-kurensa”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp