Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen wasu fitattun mutane guda biyu ga majalisar dokokin jihar Kano domin tabbatar da su a matsayin kwamishinoni da ‘yan majalisar zartarwa na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.
Wadanda aka nada su ne Barista Abdulkarim Kabir Maude, SAN wanda aka zaba daga karamar hukumar Minjibir wanda ake shirin gabatarwa a matsayin babban lauyan Nijeriya a kotun koli gobe.
Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp