• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Zulum Ya Nemi A Zuba Hannun Jari A Harkar Noman Rani

byAbubakar Abba
4 months ago
Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga Hukumar Raya Yankin Tafkin Chadi, ta zuba hannun jari a bangaren noman rani a tafkin yankin na Chadi.

Zulum ya sanar da haka ne, a lokacin da yake karbar bakuncin sabbin mahukunta na Hukumar Bunkasa Yankin Tafkin Chadi, a fadar gwamnatin jihar ta Borno da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

  • Darajar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso Shida Bisa Dari A Afirilu
  • Kudin Shigar Masana’antar Manhajojin Sin Ya Karu Da 10.8% A Watanni Hudu Na Farkon Bana

Har ila yau, gwamnan ya bukaci zuba hannun jarin, musaman a yankunan Kirenowa, Marte, Gamborun Ngala da kuma Baga.

Zulum ya yi nuni da cewa, zuba hannun jarin zai taimaka matuka da gaske, wajen bunkasa wadataccen abinci da kuma farfado da tattalin arziki a jihar da ma yankin Arewa Maso Gabashin wannan kasa baki- daya.

“Ba zai taba yiwuwa mu ci gaba da dogara kacokan a kan ruwan da muke samu ba, inda ya kara da cewa; bincikenmu ya tabbatar mana da cewa, ruwan da ake samu daga tafkin Chadi na da matukar yawan gaske, wanda idan muka mayar da hankali yadda ya kamata, ko shakka babu, za mu iya jawo ruwan ta hanyar yin amfani da injinoni,” in ji Zulum.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga.

Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, sannan kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa.

Kazalika, ya sanar da cewa, an kuma kebe karin wasu Naira biliyan 1.5, domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda a halin yanzu an kusa kammala su baki-daya.

Bugu da kari, ya bayyana cewa; bisa kokarin gwamnatinsa na mayar da hankali wajen farfado da shirin noman rani na Tafkin Chadi ta Kudu, tuni aka fara noma hekta 1,000 a karkashin aikin noma na Baga a kan kudi kimanin Naira biliyan biyu.

Gwaman ya ci gaba da cewa, har ila yau; gwamnatin jihar ta Borno ta samar da hekta 200,000 a Gamboru da kuma wata hekta 200,000 na samar da wutar lantarki a Lamboru ta hanyar amfani da tsarin ban-ruwa, domin farfado da ayyukan noma a fadin yankin baki-daya.

Haka zalika, Zulum ya sanar da cewa, gwamnatinsa ta haka rijiyoyi kusan kimanin 3,000 a Damasak da ke Karamar Hukumar Mobba.

Sannan kuma, ya yi nuni da cewa; wannan ya bai wa manoma da dama damar yin noma a fili mai tsawon kilomita 16, matakin da ya bullo da hanyar noman ruwan karkashin kasa a yankin da a baya ba a saba yin irin sa ba.

Zulum ya kuma yi alkawarin ci gaba da hada kai da hukumar, musamman domin samun nasarar fadada noman a Ngala da Damasak da sabon yankin Marte tare da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar yankin da suka dawo yankin da kuma tabbatar da dorewar samar da wadataccen abinci.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa, gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa wajen farfado da tashar famfunan ruwa da ke Chadi Basin Kirenowa.

A cewarsa, gwamnatinsa na kan kokarin ganin ganin an kafa bataliyar soji a yankin, musamman don inganta tsaro tare da samun zaman lafiya, inda ya kara da cewa; gwamnatin tasa za ta so sanin inda za a iya shiga, sakamakon cewa abubuwan da za a iya samu suna nan.

Ya kara da bayyana cewa, yana ci gaba da tuntubar shugaban kasa da sauran shugabannin sojoji, kan yiwuwar kafa bataliyar soji a Kirenowa da nufin kare tashar famfon.

A nasu jawaban daban-daban tunda farko, shugaban hukumar, Farfesa Abdu Dauda Biu da Manajan Darakta, Alhaji Tijjani Tumsa sun sanar da gwamnan cewa; an kafa sabuwar hukumar ce a ranar 13 ga watan Disamba 2024.

A cewarsu, wannan ziyara na da matukar muhimmancin gaske, duba da cewa; wuraren da ke karkashin kulawarsu, ciki har da madatsar ruwa ta Alau, na samun kulawar da ta dace.

Kazalika, sun kuma jinjina wa Zulum; kan yadda yake gudanar da ayyukansa da kuma jajircewarsa, musamman a wannan bangare na madatsun ruwa da ke wannan jiha.

Har ila yau, shugabancin hukumar ya yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar ta Borno, musamman don samun nasarar aiwatar da wadannan ayyuka da suka shafi noman rani da kiwon dabbobi da kuma kamun kifi a wadannan yankuna.

Haka zalika, sun kuma bukaci goyon bayan Gwamna Zulum, wajen ganin an kammala wannan gyara na madatsar ruwa ta Alau a kan lokaci, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi a ‘yan kwanakin baya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Wasu ‘Yan Ta’adda Dauke Da Makamai Sun Harbi Limamin Katolika A Binuwe

Wasu ‘Yan Ta’adda Dauke Da Makamai Sun Harbi Limamin Katolika A Binuwe

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version