Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya naɗa ‘yarsa ta fari, Helen Eno Obereki, a matsayin matar gwamna (First Lady) na wucin gadi, bayan mutuwar matarsa.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar, yana mai jaddada muhimmancin ofishin matar gwamna da wajibcin ci gaba da ayyukansa duk da rashin matarsa.
- Akwai Bukatar Shugabannin Arewa Su Farka – Sarkin Fawa
- Masu Kiwon Kaji Da Manoman Rogo 700 Sun Samu Horo A Jihar Edo
Gwamna Eno ya nuna ƙudirinsa na ci gaba da ayyukan tallafin zamantakewa da marigayiya matarsa ta assasa, musamman shirinta na Golden Initiative For All (GIFA) da ya mayar da hankali wajen tallafawa marasa galihu.
Yayin gabatar da ‘yarsa ga Matar Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, a lokacin da ta kai ziyarar ta’aziyya, Gwamna Eno ya nemi shawararta kan yadda za a tafiyar da ofishin matar gwamna.
Uwargidan Tinubu ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalin Gwamnan tare da tabbatar da goyon baya wajen tsara ayyukan ofishin matar gwamnan jihar tare da nata.