A ranar Talata, gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya rantsar da wasu ƙarin manyan masu ba shi shawarwari a ɓangarori daban-daban da nufin kyautata gudanar da mulki da tabbatar da manufofi da tsare-tsaren gwamnati mai ci sun aiwatu yadda aka tsara.
Da ya ke rantsar da su a gidan gwamnatin jihar, Bala Muhammad ya lura kan cewa an yi naɗe-naɗen ne da nufin sanya mutanen a wurare daban-daban domin su ma su yi amfani da gogewarsu da ƙwarewarsu wajen ganin sun taimaka wa gwamnati mai ci wajen cimma kyawawan manufofin kyautata rayuwar al’ummar jihar.
- Gwamnatin Kano Ta Janye Ƙararrakin Da Aka Shigar A Kan Masu Zanga-Zangar #EndBadGovernance
- An Maka Gwamna Fintiri A Gaban Kotu Kan Ƙirƙiro Sabbin Masarautu A Jihar Adamawa
Don haka ne ya yi kira ga sabbin Mashawarta nasa da kasa su bai wa marar ɗa kunya ta hanyar gudanar da aiki tukuru da ba shi shawarwarin da za su ciyar da jihar da al’ummarta gaba.
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu.
Sauran sun haɗa da Alh. Danladi Mohammed Danbaba, babban mai bada shawara kan harkokin jin-ƙai; Hon. Sani Mohammed Burra, babban mai bada shawara kan harkokin majalisar dokokin jihar da na tarayya; Hon. Yakub Ibrahim Hamza, babban mai bada shawara kan ilimi mai zurfi da kuma Hon. Shitu Zaki da ya zama babban mai bada shawara kan harkokin siyasa.
Ƙarashin su ne Usman DanTuraki, babban mai bada shawara kan kan harkokin kungiyoyin kwadago; Farfesa Simon Madugu Yalams, mashawarci kan harkokin fasaha da koyar da sana’o’i sai kuma Abubakar Abdulhamid Bununu, mai bada shawara kan haɗin kai jama’a da yankuna.
Yayin da yake taya waɗanda ya nada murna, gwamna Bala Muhammad ya horesu da su nuna kwazo da kamala, dattako da sanin ya kamata yayin da suke hidimtawa jama’an jihar.
Ya nuna kwarin guiwarsa a kansu da cewa tabbas yana da yaƙinin gudunmawarsu zai taimaka sosai wajen cimma nasarori da manufofin gwamnatin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp