Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya yi wa fursunoni 96 aka daure kan laifuka daban-daban a gidajen gyaran hali a jihar afuwa.
Gwamnan ya ba su kyautar Naira dubu 100 kowannensu da nufin su yi amfani da kudin wajen neman sana’ar da za su yi idan sun koma cikin al’umma.
- Wuraren Kiwo: Fulani Sun Yi Murna Da Matakin Shugaban Kasa – Ngelzarma
- Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa 2 Sun Mutu A Yayin Turmutsutsun Karɓar Abincin Tallafi
Gwamnan, wanda ya yi amfani da karfin ikon da doka sashe 212 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ya ba shi karkashin yin afuwa.
A yayin jawabinsa, gwamna ya ce, ya yi afuwar ne bisa shawarwari da kwamitin bayar da shawara kan yin afuwa na jihar ya yi, biyo bayan bibiyar zamantakewar fursunonin a gidan gyaran hali da kuma irin tuba da nadamar da suka yi kan laifukan da aka same su.
A cewar gwamnan, wadanda kwamitin ya yi la’akari da su wajen ganin an sake su sun hada da masu yawan shekaru, fursunoni masu dauke da cututtuka da ka iya yaduwa, da kuma wadanda aka yi musu daurin rai da rai amma sun shafe sama da shekaru sama da 10 a tsare tare da nuna nadama da ake da fatan za su kasance masu amfani idan suka koma cikin al’ummominsu.
Sannan, gwamnan ya biya kudin tara da aka yanke wa wasu da nufin su samu fita daga daurewar da aka musu.
Sai dai a cewarsa, kwamitin ya yi fatali da bukatar wasu da suka aikata manyan laifuka, inda aka ki amincewa da fito da su.
Muhammad, ya hori wadanda ya sanya hannu aka sake su da su kasance mutane na kwarai kana su tabbatar ba su koma rayuwarsu na bayae da ya kai su ga shiga gidan yari ba.
“Kan halin da kasar nan ke ciki, kowane daga cikinku za a ba shi naira dubu 100, ina jan hankalinku da ku yi amfani da kudaden ta hanyar da ya dace. Kudin ba daga aljihuna ba ne, daga aljihun jiha ne.”
Gwamnan jihar ya bukaci babban jojin jihar da ta taka wa alkalai musamman alkalan da suke kananan kotuna da su daina yawan jibge mutane a gidajen yari kan wasu ‘yan laifukan da ba su kai a gungunta wa mutum rayuwarsa a gidan yari ba.
Shi kuma a jawabinsa, shugaban kwamitin yin afuwa kuma kwamishinan shari’a na Jihar Bauchi Hassan U. El-Yakub (SAN), ya ce gwamnan ya amince da fitar da kudi sama da naira miliyan bakwai domin biyan kudaden tara da kotuna suka yanke wa fursunonin kan laifukan da suka aikata.
Sannan, ya ce gwamnan ya kuma sake amincewa da fitar da wani kudi da yawan su ya kai Naira miliyan 13 da za a raba wa fursunonin da aka saki a matsayin tallafi da kudin mota domin su koma gidajensu domin ci gaba da kasance masu amfani a cikin al’umma.
“Kwamitin bayar da shawara kan afuwa ya amshi bukata daga wajen fursunoni 106 da suke rokon yafiyar gwamna. Amma kwamitinmu ya kai ziyara zuwa gidajen yari da suke Bauchi, Alkaleri, Azare, Bogoro, Burra, Darazo, Ningi, Zaki, Gamawa, Misau, Shira, Toro, Tafawa Balewa da Jama’are, inda aka karshe kwamitin ya amince da bukatar fursunoni 96 kuma cikin tausayawar gwamna ana gabatar masa ya amince.”
A nasu jawaban daban-daban kwanturolan hukumar kula da gidan yari a jihar Bauchi, Ali Bajoga, kwamishinan ‘yansanda na Jihar Bauchi Auwal Musa da sauran sun jinjina wa gwamnan bisa yin afuwar, sun kuma nuna hakan zai kara rage cunkoson da ake fama da shi a gidajen gyaran hali a jihar.
Wasu daga cikin fursunonin da aka sake su, sun nuna godiyarsu tare da daukar alkawarin ba za su sake komawa rayuwarsu ta baya ba.