Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya zama shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP na kasa baki daya.
Bala wanda ya samu nasarar dare kujerar ne a wani taron da zababbun gwamnonin suka gudanar a Jihar Bauchi da ya samu halartar Gwamnonin tare da Atiku Abubakar.
- Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari
- Abba Gida-Gida Ya Ba Da Umarnin Rushe Gine-Ginen Da Aka Yi A Filayen Gwamnati
Da yake sanar da sakamakon zaben nasu, gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce, sun cimma matsayar ne bisa lura da cewa Bala Muhammad zai iya jagorantar kungiyar yadda ya kamata.
Talla
Kazalika, ya sanar da cewa gwamnonin PDP din sun kuma zabi gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.
Talla