Gwamnan jihar California dake kasar Amurka Gavin Christopher Newsom, ya ce matakin kara haraji da gwamnatin Trump ke aiwatarwa ya haifar da babbar illa ga jihar California, amma duk da haka jihar za ta ci gaba da bude kofarta ga kasar Sin domin gudanar da kasuwanci.
Newsom ya bayyana hakan ne yayin zantawa da wata kafar watsa labarai ta kasar Japan, yana mai cewa, California ta dade tana abotar cinikayya tare da Sin. Kuma bangarorin biyu sun sa hannu kan jerin yarjeniyoyin hadin gwiwa tsakanin jihohi, da gundumomi da kuma biranensu.
- Mun Fara Shirin Lashe Firimiya Ta Gaba –Slot
- Tsohon Shugaban NNPC, Kyari Ya Musanta Zargin Faɗawa Tarkon EFCC
Ya ce, yayin da ya kai ziyarar aiki kasar Sin a shekarar bara, ya yi nasarar yaukaka dangataka tsakanin jiharsa da Sin zuwa mataki na kasa. Jihar California ta bude kofa ga dukkan abokan ciniki, ciki har da Sin, kasancewar hada-hadar cinikayyar duniya ba batu ne na wasa ba, dukkan bangarori suna dogaro da juna.
Yayin da aka tabo batun manufofin cinikayya da gwamnatin Trump ta dauka, Newsom ya ce, dalilin da ya sa ya soki matakan na gwamnatin Trump shi ne, jihar California ta fi fama da mummunan tasirin da manufofin suka haifar sama da sauran jihohin kasar.
Tun bayan da shugaba Trump ya sanar da matakin kakaba haraji a watan Afirilu, Newsom ta yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da ke wajen Amurka, da kada su sanya harajin ramuwar gayya kan kayayyakin da ake fitarwa daga jihar California. Kazalika, California ce jihar farko da ta kai karar gwamnatin Trump kan batun harajin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp