Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya gargaɗi kwamishinoninsa da kada su je wajen aiki ba tare da saka irin hular da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke sakawa ba.
Gwamnan ya yi wannan magana ne yayin da yake rantsar da wasu sabbin kwamishinoni, inda shi ma yake sanye da irin wannan hula.
- Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP
- ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako
A cewarsa: “Kun ga wannan hular? Ba zan yafe wa duk wanda ya zo aiki ba tare da ita a kansa ba.”
Ya ƙara da cewa, “In dai tufafinka na al’ada ne da ke buƙatar sanya hula, dole ne ka saka irin wannan hular.”
Gwamna Okpebholo ya ce duk kwamishinan da ya karya wannan doka zai tafi gida.