Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya umarci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka kai harin ranar Lahadi a kauyukan Mangu da kananan hukumomin Bokkos na jihar.
Gwamnan ya bada umarnin ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na jihar, Dokta Makut Maham ya fitar ranar Litinin a Jos.
- An Kashe Mutane Da Dama, Aka Kone Gidaje A Rikicin Makiyaya Da Manoma A Filato
- Ma’aikatan Filin Jirgin Saman Legas Sun Shiga Yajin Aiki
Ya ce yin gaggawar shiga tsakani da hukumomin tsaro za su yi zai shawo kan tabarbarewar lamarin tare da tabbatar da gudanar da adalci ba tare da bata lokaci ba.
Lalong ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a yankin Murish da gundumar Kumbum da kuma Jwak Mai tumbi a karamar hukumar Mangu da kuma Marish a karamar hukumar Bokkos wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya bayyana hare-haren a matsayin wani yunkuri na sake dawo da zamanin tashe-tashen hankula wanda aka yi fama da shi biyo bayan makudan kudaden da Gwamnati ta kashe wajen samar da tsaro, samar da zaman lafiya da sulhu.
Da yake jajantawa wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu, gwamnan ya umarci hukumar samar da zaman lafiya da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da su gaggauta kai dauki ga wadanda lamarin ya shafa domin tallafa musu.