Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya amince da nadin Ibrahim Isa na Gidan Rediyon BBC a matsayin Babban Daraktan Kafar Yada Labarai ta Jihar Gombe (GMC).
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya sanar da amincewar gwamnan, yana mai cewa nadin na Ibrahim Isa, wadda ya fara aiki nan take, ya samo asali ne daga nagartattun halaye da kwarewarsa a fannin yaɗa labarai.
- Matsin Rayuwa: Magidanta 106 Suka Daina Kula Da Iyalansu A Gombe Cikin 2023 – NHRC
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Kwamitin Asusun Samar Da Tallafin Tsaro
Ibrahim Isa, yana da kwarewar aikin jarida ta fiye da shekaru ashirin, hakan ya sa ya yi fice a matsayin dan jarida mai tura rahotanni, mai haɗa labaru da karanta su, kuma mai gudanar da shirye-shiryen talabijin kana manajan watsa labarai.
Duba da gogewa da kwarewarsa, ana sa ran Ibrahim Isa zai yi amfani da sabbin dabaru da hikimomi a Hukumar Yada Labarun ta Jihar Gombe don inganta harkokin yada labarai, kamar yadda kakakin gwamnan Malam Ismaila Uba Misilli ya nakalto.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa jagorancin Ibrahim Isa zai taimaka wajen bunkasar kafar yada labaran ta GMC da yi wa al’umma hidima ta hanyar samar musu sahihan labarai da suka dace.
Har ila yau, Gwamna Inuwa Yahayan ya amince da daga darajar Dakta Ishiyaku Babayo Ibrahim, daga matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) kan hadin gwiwa da abokan huldar ci gaba zuwa mai ba da shawara na musamman kan wannan fanni.
Sanarwar hakan wacce Sakataren Gwamnatin Jihar ya sanar, ta ce an dauki matakin ne duba da irin nasarorin da Dr. Ibrahim ya cimma, da jajircewarsa na musamman da kuma tasirin da ya yi cikin ɗan kankanin lokaci daga nada shi a matsayin mai bada shawarar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa daga darajarsa zuwa mukamin mai ba da shawara na musamman zai kara habaka shirye-shiryen hadin-gwiwa na jihar tare da kara kaimi wajen samar da kudade da tallafi daga bangarori daban-daban na ci gaba don ba da gudummawa ga jin dadi da ci gaban Jihar Gombe baki daya.