• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Gombe Ya Nada Mai Rikon Safiyo-Janar Da Babban Jami’in Kididdiga

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Gwamna Inuwa Ya Bukaci Musulmai Su Ci Gaba Da Habbaka Darussan Ramadana
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Zakari Isa Kwami a matsayin mai rikon mukamin Safiyo-Janar da Ibrahim Abubakar Dule a matsayin mai rikon kwarya na babban jami’in kididdiga na Jihar Gombe. 

Shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Bappayo Yahaya ne ya sanar da amincewar Gwamnan, yana mai bayyana cewa hakan ya biyo bayan ritayar da masu rike da mukaman biyu suka yi ne, kuma ya dace da ikon da aka bai wa gwamna a sashi na 208 karamin sashi (2c) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka yi wa kwaskwarima.

  • Zaben Gwamnan Adamawa: Kotu Ta Kori Karar Da Binani Ta Kai INEC

Ya ce, sabbin nade-naden an yi su ne bisa la’akari da cancanta, aminci da sadaukar da kai da kuma kwarewar da suke da shi a aikin gwamnati, inda ya bukace su da su sanya irin wadannan halaye da kwarewa nasu wajen gudanar da ayyukan su a sabbin mukaman nasu.

Labarai Masu Nasaba

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Sabon Mukaddashin Safiyo-Janar din Zakari Isa Kwami, ya yi karatun digirin sa a harkar safiyo a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, kuma ya fara aiki ne a shekarar 2006 a matsayin jami’in filaye kuma ya yi rajista da kungiyar kwararrun safiyo-safiyo ta Nijeriya wato Surveyors’ Council of Nigeria (SURCON) a shekarar 2017. Ya rike mukamai daban-daban har ya kai matsayin babban safiyo na jiha.

A nasa bangaren, mukaddashin babban jami’in kididdigan na jiha, Ibrahim Abubakar Dule, ya yi digirin sa ne a jami’ar Abuja. Ya kuma fara aiki a Jihar Gombe ne a shekarar 2005 a matsayin magatakardan kungiyoyin hadin kai, inda ya yi ta samun karin girma har zuwa matsayin babban magatakardan kungiyoyin hadin kai, daga nan kuma ya koma ofishin kididdiga na Jihar Gombe a matsayin babban jami’in kididdiga.

Dukkanin nade-naden sun fara aiki ne daga ranar 6 ga wannan wata na Afrilun 2023.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

ISWAP Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai 3 Da Masu Tsaro 2 A Borno

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Yi Dirar Mikiya Wurin Taro, Sun Kashe Shugaban Al’umma A Imo 

Related

Labarai

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

2 hours ago
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

3 hours ago
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC
Labarai

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

6 hours ago
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

8 hours ago
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
Labarai

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

11 hours ago
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

12 hours ago
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 Da Sojoji 2 A Jihar Benuwe

'Yan Bindiga Sun Yi Dirar Mikiya Wurin Taro, Sun Kashe Shugaban Al'umma A Imo 

LABARAI MASU NASABA

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.