Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da nadin Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar (SSG).
A wata sanarwar da babban Sakataren fadar Gwamnatin jihar Gombe, Barista Balarabe Poloma ya fitar a ranar Alhamis, ya nakalto cewa, gwamna Inuwa ya kuma amince da nada Ismaila Uba Misilli, a matsayin darakta-janar kan harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jarida.
Kazalika, Inuwa ya kuma nada Dakta Mu’azu Shehu, a matsayin darakta-janar na Sashin bincike da taskace bayanai.
A cewar sanarwar dukkanin nade-naden sun fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Yunin 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp