Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya aike da sunayen zababbun kwamishinoni 17 ga majalisar dokokin jihar domin tantance su.Â
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne, ya mika sunayen ga akawun majalisar Barista Rukaiyatu A. Jalo, ga kakakin majalisar.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 59, Sun Ceto Mutum 88
- CBN Ya Kara Kudin Ruwa Mafi Tsada A Cikin Shekara 22
Zababbun Kwamishinoni su ne: Abdulkadir Mohammed Waziri, daga karamar hukumar Akko; Adamu Inuwa Pantami, Gombe; Barista Zubairu Mohammed Umar, Funakaye; Dakta Abdullahi Bappah Garkuwa, karamar hukumar Gombe da kuma Dr. Aishatu Umar Maigari da aka zabo daga karamar hukumar Dukku.
Sauran su ne: Dakta Barnabas Mallet, Kaltungo; Dr. Habu Dahiru, Yamaltu-Deba; Dr. Usman Maijama’a Kallamu, Kwami; Hon. Asmau Iganus, Shongom; Lt. Col. Abdullahi Bello (ritaya) Balanga hadi da Mijinyawa Ardo Tilde, karamar hukumar Funakaye.
Har ila yau akwai: Mohammed Shettima Gadam, Kwami; Mohammed Gambo Magaji, Dukku; Mohammed Saidu Fawu, Billiri; Nasiru Mohammed Aliyu, Yamaltu-Deba; Salihu Baba Alkali, daga karamar hukumar Nafada sai Sanusi Ahmed Maidala, da gwamnan ya zabo daga karamar hukumar Akko.