Gwamna Malam Umar A. Namadi ya bayar da umarnin dakatar da Kwamishina Auwalu Dalladi Sankara, kan zargin aikata lalata da matar aure.
Dakatarwar ta fara aiki nan take, bayan zargin kama shi da hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi.
- Nazarin Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (10)
- Bikin Ranar Sikila: Yara 138,000 Ake Haihuwa Da Cutar A Duk Shekara –Dr. Kangiwa
A cikin wata sanarwa da Malam Bala Ibrahim, Sakataren Gwamnatin Jihar, ya fitar, an bayyana cewa wannan mataki yana nuna kudirin gwamnatin wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.
An bayyana dakatarwar a matsayin wani mataki domin tabbatar da adalci yayin da ake gudanar da binciken, tare da jaddada muhimmancin kiyaye amincewar al’umma da shugabanci na gaskiya.