Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya gabatar da kudurin kasafin kudin 2026 na Naira biliyan 901.8 ga majalisa a ranar Talata a zauren Majalisar Dokoki ta Jihar da ke Dutse, babban birnin jihar.
A yayin gabatar da kudurin, gwamnan ya samu rakiyar manyan mutane, ‘yan siyasa, sarakuna, masoya APC daga kowane lungu, da kungiyoyi masu zaman kansu, da ke goyon bayan shirye-shiryen gwamnan jihar.
Namadi yayin da yake gabatar da kasafin kudin ga Majalisar Dokoki ta Jihar, cikin farin ciki da kwarin gwiwa, ya bayyana cewa, “Wannan kudurin kasafin kudin na Naira biliyan 901.8 ba adadi ne kawai ba, taswirarmu ce ta sauya Jigawa ta hanyar samar da ababen more rayuwa, ilimi, da ayyukan yi, tare da tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya a tafiyarmu ta samar da wadata da ci gaba.
“Mun fifita noma da tsaro don karfafa ribar da muka samu, muna gayyatar dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da wannan kasafin kudin ya zama gaskiya da nasara ga mutanenmu.”
A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Dangyatim, bayan ya karɓi kundin kasafin kuɗin na shekarar 2026 sannan kuma ya tafa wa gwamnan, ya ce, “A madadin wannan majalisar, muna maraba da wannan shawara mai cike da kaifin basira wacce ta fi mayar da hankali kan haɓaka rayuwar jama’a, za mu yi nazari sosai don samar da mafita cikin sauri ga makomar Jigawa mai haske.”














